Connect with us

Labarai

A Kawo Mana Daukin Gaggawa Kafin Faduwar Damuna – Fulanin Bagwai

Published

on

IMG 20220312 WA0041

Daga Umar Lawan Tofa

 

Al’ummar kauyen Kojele da kewaye a yankin karamar hukumar Bagwai dake a jihar Kano, sun zargi ‘yan siyasa da yunkurin hada Fitina tsakanin su da manoma a yankin ta hanyar sayar da Burtalolin da suke kiwon Dabbobi.

 

Yusufa Fulani Kwajale Rugar Dawaki,wanda shi ne Sarkin Fulanin yankin yace suna da yawan Dabbobi amma an sayar da mafi yawa daga wuraren kiwon kuma basu da wata sana’ar da ta wuce kiwo.

 

Yusufa Fulani Kojele, yace basu da wani wurin kiwo illa wuraren da suka tarar iyaye da kakannin su suna yi, amma yanzu ‘yan siyasa sun sayarwa wasu mutanen daban.

 

Yace garuruwan fulanin da matsalar ta shafar sun hada da Dakatawa da Yolere da Medawa da Kojele da Tuga da Kariya Rimin Bai da Kariya mai Kambu da Daneji da kuma Rugar Mace

 

A nasa bangaren jagoran samarin Fulanin yankin Tukur Ahmad yace an gama sayar da Burtalai da suke kiwo basu da madafa.

 

”kuma idan sun kai korafi wurin Kansila ko Dagaci duk sai su ce basu da sa hannun akan wannan lamari to mu kuma wannan abin yana damun mu”

”Gwamnati ita ta ke da hakki akan komai don Allah don Annabi ta taimaka ta duba mana wannan matsàla, sannan wannan wuraren da aka gama saidawa anan muke kiwo mu sami abinda zamu ciyar da iyalan mu, sannan idan muka kai koke wurinta ita da ta riga ta wassafa wannan wurin, hasalima wani lokacin idan muka kawo koken mu tana iya hada kai da kamar wadanda suka sayi wurin su rika mara musu baya wani lokacin ma akan iya ci mana zarafi akan cewar mu masu Dabbobi mu ne bamu da adalci”

 

”To mu rashin adalcin mu a nan shine guda daya, ba a fitar mana da wurin da zamu yi kiwo ba, inda muka tarar tun kakannin mu suna yi rana tsaka yanzu anzo an gama yayyankawa an an saida su, min kai koke har karamar hukuma amman abin ya faskara”

 

Shi ma wani wakilin Fulanin, Abdulmumini Ayuba Jaulere ya yi ce an yi musu kwace na Burtalai kuma sun kai kuka matakai daban-daban.

” Kasar Kojele ko Bagwai gaba daya an keta mana haddin makiyaya, saboda haka muke kai korafi daga matakin daya bayan daya amma wadanda suka sayar da wuraren nan sun ce bamu iya a fitar mana da burtalolin nan ba.

Saboda haka mu din nan fa haifaffun Najeriya ne, ‘yan jahar Kano ne, ku mun yi biyayya duk iya yadda ake tsammani amma anki”

 

”Matasa suna neman idan damuna ta fadi kowanne matashi makiyayi suna barazanar zasu dauki mataki a hannun su, zai dauki hukunci a hannun sa, to shi ne mu iyayen fulanin manyan dattawa muka ce kafin a kai ga wannan matsayin ya kamata hukuma ta duba, don za a iya haifar abinda bai dace ba.

‘Saboda yaran mu gaba daya kowanne target ya ke yi a kullum na damuna ta fadi duk yadda za ai ayi, saboda haka a gaggauta kawo mana dauki da taimako na hukuma”

Wakilin jaridar Independent post ya yi kokarin jin ta bakin shugaban karamar hukumar ta Bagwai Alhaji Inuwa Dangada. amma hakan bata samu ba, kasancewar ya kira shi a wayar salula yace yana Kano, sannan muka aike masa da sakon tes, amma har zuwa lokacin da muka wallafa wannan rahoto bai ce koma bai.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *