Labarai
Fernandinho ya yanke shawarar bari Manchester city.

Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Manchester city, Kuma Dan wasan kasar Brazil Fernandinho zai bar kungiyar tasa a karshen wannan kakar wasan.
Dan wasan na son komawa kasar sa ta Brazil ne domin cigaba da taka leda.
Fernandinho ya tabbatar da hakan ne bayan shawara da iyalan sa, sannan ya sanar da kungiyar tasa ta Manchester city hukin cin nasa.
A wani bangaren Kuma kocin kungiyar tasa ta Manchester city ya nuna rashin jin dadin sa da jin sanarwar ta Dan wasan nasa.
Inda yace yaso ace Dan wasan ya tsawaita kwantiragin sa zuwa wata kakar wasannin.