Labarai
Babu amincewar shugaban kasa kan Karin albashin masu mukaman siyasa da alƙalai

Mun samu labarin da ke yawo cewa an yi ƙarin kashi 114 cikin 100 na albashin shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, zaɓaɓɓun masu riƙe da muƙaman siyasa na tarayya da na jihohi da kuma jami’an shari’a.
Wannan labari ne mara tushe domin babu inda Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da batun ƙarin albashin, kuma babu inda aka gabatar da wannan ƙudiri a gabansa domin neman yardarsa.
Duk da cewa yana cikin kundin tsarin hukumar tattara kuɗin shiga da tsara kasafin kuɗi ta ƙasa RMAFC su ba da shawarar daidaita albashi da alawus ga masu rike da muƙaman siyasa da alƙalai, saidai hakan ba zai iya aiki ba har sai shugaban ƙasa ya yi duba tare da amincewa da shi.
Sannan kuma hukumar RMAFC, ta hannun Manajan Hulda da Jama’a, ta mayar da martani kan wannan labari na ƙarya da ake yaɗawa, ta kuma bayyana gaskiyar al’amarin.
Wannan labari mara tushe ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta da kuma wani ɓangare na kafafen yaɗa labarai, wanda hakan ya ƙara haifar da hatsarin da labaran karya ke haifarwa ga al’umma da kuma cigaban ƙasa baki ɗaya.
Ba shakka, an kirkiri wannan labarin karyar ne don mugun nufi ga sabuwar gwamnati, da nufin kawo tarnaƙi akan yunƙurin da ake yi na samar da gyara, da kuma kyakkyawar sheda da gwamnatin Tinubu ke ci gaba da samu a tsakanin ƴan Najeriya a halin yanzu, sakamakon tafiyar da manufofinta cikin tsari mai inganci da zai samar da cigaba.
Ya kamata ‘yan jarida, kafofin yaɗa labarai, da jama’a duka su fahimci cewa duk labarin ayyukan gwamnati da batu akan manufofin ta da ba su fito a hukumance ba, labari ne mara tushe da yakamata a yi watsi da shi.
Ana kuma umartar ma’aikatan watsa labarai, a kowane lokaci, su dinga binciko tushen labaransu don tabbatar da sahihancin labaran da suke yaɗawa, wanda hakan shine alamar aikin jarida na ƙwarai.