Labarai
Abba Kabir Yusuf ya karbi shaidar lashe zaben gwamnan Kano daga INEC

Hukumar zabe Mai zaman kanta ta kasa INEC ta Mika Takardar shedar lashe zaben gwamnan jihar Kano ga Engineer Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP.
An gudanar da bikin Mika Takardar shedar ne yau Laraba a shalkwatar hukumar zabe ta INEC Dake nan Kano gaban dubban daruruwan magoya baya.
A yayin bikin, an kuma Mika takardun shedar lashe zabe ga mambobin majalisar dokokin jihar Kano.
Taron ya gudana cikin kasaitaccen yanayi da matakan tsaro.
Abin da zababben gwamnan na Kano ke Jira yanzu shi ne rantsuwar kama aiki ranar 29 ga watan Mayu Mai zuwa.