Labarai
Adadin mutanen da suka mutu a sabon rikicin Filato ya haura 100

Yawan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon rikicin da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a jihar Filato da ke Najeriya, ya zarce mutane 100, kamar yadda mahukunta suka tabbatar a ranar Juma’a.
Bayanai sun ce akwai fargabar adadin mamatan ka iya karuwa la’akari da cewar ana cigaba da laluben dazukan da ke zagaye da yankin da tashin hankalin ya auku a karamar hukumar Mangu.
Shugaban karamar hukumar, Minista Daniel Daput ya ce ya zuwa ranar Juma’a an yi jana’izar binne gawarwakin mutane kimanin 50, za kuma a binne wasu karin 50 a ranar Asabar.
Rikicin dai ya fara ne tun daga ranar Talata ranar 16 ga watan Mayu, bayan harin da gungun ‘yan bindiga suka kai kan wasu kayukan karamar hukumar ta Mangu, inda suka kone gidaje da dama, baya ga kashe akalla mutane 20, akasarinsu mata da kananan yara.
Wani makiyayi mai suna Bello Yahya, ya ce harin ‘yan bindigar ramuwar gayya ce akan kashe wani makiyayi tare da dabbobinsa da wasu manoma suka yi a watan da ya gabata, a lokacin da makiyayin ya yi musu barna a gonakinsu.