Labarai
AKK PROJECT: Gwamnatin Kano Ta Yi Alkawari Yin Adalci Ga Dukkan Wadanda Aikin Ya Shafa

Kwamishinan Kasa Da Safiyo Na jihar Kano Alhaji Adamu Aliyu Kibiya ya jaddada kudirin gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf na yin adalci ga kowanne mutum ba tare da nuna banbanci ba.
Kwamishinan na Bada wannan tabbaci ne yayin ganawa da manema labarai bayan da ya karbi korafin al’ummar yankin Tamburawa da kewaye wadanda aka yi amfani da gonakin su don gina cibiyar da Depo na Iskar gas da akewa lakabi da AKK GAS PROJECT da gwamnatin Tarayya ke ginawa a Nan Kano.
”Kamar yadda suka Sani, wannan aiki ne na gwamnatin Tarayya, saboda haka za ayi aikin, ba zai tsaya ba. Kuma naji dadi Alhamdulillah duk cikin koke-koken su dama Basu ce ba za ayi ba naji dadi da suka fahimci abin cewar su basa korafi kan aikin”
Ya ce sun gabatar masa da korafi ne kan neman adalci amma ba adawa da aikin ba, Kuma duk korafe-korafen su na batun biyan diyya ne.
Alhaji Adamu Aliyu Kibiya ya Bada tabbaci cewar gwamnati zata duba koken su bayan gudanar da bincike Kuma duk Wanda aka tauye hakki za a bi masa.
Ya tabbatar wa da al’ummar jihar Kano cewar za a duba dukkan korafe-korafen da ma’wikatar ta karba Kuma Babu Wanda za a zalunta.
To sai dai ya ce hankalin masu korafin kan cewar wasu daga cikin su suna gaban kotu kan batun, Inda ya ce ma’aikatan sa zata duba wadanda maganar su Bata gaban kotu ne kawai domin ba zai shiga hurumin kotu ba.
”Akwai wadanda suke gaban kotu daga cikin masu korafin, saboda haka bamu da hurumi mu Yi Wani abu kan wannan domin ba zamu shiga hurumin kotun ba. Amma wadanda maganar su Bata gaban kotu zamu Yi bincike kan batun”
A jawabin su tun farko jagororin kungiyar dake fafutukar neman adalci akan gonakin na su, sun roki gwamnatin da ta soke Shirin da aka Yi na Gina rukunin masana’antu da na gidajen ma’aikata da gwamnatin Kano a baya tace zata yi a wurin.
Da yake magana, jagoran dattawan kungiyar Malam Isah Yusuf Kumbotso yace gwamnatin bayan ta kirkiro aikin ne kawai don ta zalunce su a kwace musu gonaki.
Yace gonaki sune dukiyar da manoman ke alfahari da su kuma raba su da su babban tashin hankali ne ga rayuwar su