Connect with us

Labarai

Al-Nassr ta gaza lashe gasar kwallon Saudiya duk da sayen Ronaldo

Published

on

SWUGVCQH5BMCNGDQPD3QIAMBQ4 1 scaled

Kungiyar Al-Nassr ta gaza lashe kofin gasar kwallon kafar Saudiya, duk da ware miliyoyin dalar da ta yi wajen kulla yarjejeniya da Cristiano Ronaldo, jim kadan bayan rabuwarsa da Manchester United.

Fatan Ronaldo da kungiyar ta sa ta Al-Nassr na zama zakara a kakar wasa ta bana ya zo karshe ne a ranar Asabar da ta gabata, bayan da abokiyar hamayyarsu Al-Ittihad ta samu nasarar doke Al-Feiha da kwallaye 3-0, abinda ya ba ta damar lashe kofin gasar Saudiya, karo na farko tun shekarar 2009.

A karshen shekarar bara Ronaldo ya raba gari da Manchester United, ‘yan kwanaki bayan wata hira da yayi, wadda a cikinta ya caccaki shugabannin kungiyar da ya ce sun ci amanarsa, zalika kocinsa a wacccan lokaci Erik ten Hag ba ya mutunta ta shi, dan haka shi ma bay a ganin kimarsa.

A shekarar ta bara, Al-Nassr ta ware dala miliyan 214 wajen kulla yarjejeniya da Ronaldo, har zuwa shekarar 2025, abinda ya sanya fitacciyar mujallar Forbes ta bayyana shi a matsayin dan wasan da ya yi wa takwarorinsa na kowanne fanni fintinkau wajen daukar albashi mafi tsada.

Yayin da ya rage wasa daya a kammala gasar kwalon kafar Saudiya, Ronaldo ya ci wa Al-Nassr kwallaye 14 cikin wasanni 16 da ya buga mata.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *