Labarai
Al’ummar Unguwar Tunga Sun Kai Kukan su Hukumar KEDCO kan rashin samun hasken lantarki

Alummar Unguwar Tunga dake karamar Hukumar Gwale a jihar Kano Sun Kai kukansu kamfanin rarraba hasken wutar lantarki ta KEDCO dake jihar Kano don nuna damuwarsu kan halin matsin da suka tsinci kansu sakamakon karancin hasken wutar lantarkin da suke fama da ita.
Da yake jawabi lokacin da alummar unguwar suka yi zuwa dandazo zuwa ofishin kamfanin kedcon da ke unguwar chiranchi kan titin zuwa fanshekara shugaban Ayarin Alhaji Ahmad Ango yace rashin samun hasken wutar lantarkin ya jefa alummar unguwar cikin halin kaka nikayi.
Ya ce duk da cewa alummar unguwar na da himma wajen biyan kudin wuta, amma abin takaici shine yadda kamfanin na kedco ya mayar da unguwar ta Tunga saniyar ware a fannin ba da hasken wutar lantarki.
Da kyar ake bamu wutar minti 30 a cikin awa 24,bayan unguwannin da ke makwabtaka da mu irinsu janbulo, dorayi karama, unguwar Bello, kabuga kullum cikin samun hasken lantarki suke, me mutanen tunga suka yiwa kedco ne a basa samun wutar?” inji Malam Ahmad Ango.
Ya ce munzo ne da korafinmu a rubuce, kuma muna bukatar shugabancin kamfanin kedco mai Adalci ya shigo cikin wannan batu don kawowa alummar Tunga doki.
Da take jawabi a madadin kamfanin kedco wata jami’ar kamfanin mai suna Hajiya Fauziya tace za su duba lamarin kuma zaa sami maslaha.