Connect with us

Labarai

An Gargaɗi Al’umma Kan Amfani Da Ruwan Sama

Published

on

images 2 18

A yayin da yanayin damina ke ci gaba da kankama, an buƙaci al’ummar jihar Kano da su kula sosai wajen amfani da ruwan sama a wajen sha da sauran ayyukan yau da kullum.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya yi gargaɗin a cikin wata sanarwa da ta fito daga sashin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, mai ɗauke da sa hannun shugaban sashin, Ibrahim Abdullahi, aka raba wa manema labarai.

Kwamishinan ya ce lokacin saukar ruwan sama lokaci ne da ke tattare da hatsari na samuwar cutar amai da gudawa wanda tuni wasu jihohi a Najeriya sun gamu da matsalar, yana mai cewa wannan dalili ne ya sa wajibi a ja hankalin alumma da cewa rigakafi ya fi magani.

Dakta Labaran ya ci gaba da cewa wajibi ne mutane su kula da abin da za su ci da wanda za su sha, musamman kayan lambu, kayan marmari da kuma ruwan sha, ya ƙara da cewa tilas jama’a su kula da waɗannan ƙwarai da gaske domin kar a ci ko a sha gurɓataccen abinci ko ruwa.

“Yana da kyau mutane su fahimci cewa, ruwan saman da ake yi a farkon damina ba mai kyau ba ne. Idan ya zama dole sai an yi amfani da shi, to a tabbata an yi amfani da dukkan sinadaran tsaftace ruwa; a dafa a tace kafin a yi amfani da shi. Yin haka zai taimaka sosai wajen hana kamuwa da cutar amai da gudawa”, ya ja hankalin al’umma.

Kwamishinan ya kuma ja hankalin jama’a wajen amfani da kayan lambu da na marmari, inda ya ce wajibi su ma a tabbatar an wanke su sosai da ruwa mai tsafta kafin a yi amfani da su kasancewar sayo su ake yi daga kasuwa ba tare da cikakkiyar tsafta ba.

Daga nan sai ya tabbatar da ƙudirin gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf na ci gaba da kula da lafiyar al’ummar jihar Kano a ko da yaushe, kasancewar fannin lafiya na ɗaya daga ɓangarorin da Gwamnan ya bai wa muhimmanci.

Daga ƙarshe, Dakta Labaran ya ja hankalin al’umma da kada su yi ƙasa a gwiwa wajen ziyartar asibiti mafi kusa yayin da duk aka kamu da rashin lafiya, yana mai addu’ar Allah Ya kiyaye jihar Kano da al’ummarta, “Amma fa wajibi sai mun kiyaye kanmu, sannan Allah zai kiyaye mu.”

Sa hannu:
*Ibrahim Abdullahi*
Jami’in Yaɗa Labarai
Ma’aikatar Lafiya
21 ga Yuni 2024

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *