Connect with us

Labarai

Ba Da Gaske Sha’aban Yake Takara Ba, Shi Yasa Na Koma Gawuna – Rarara

Published

on

images 5 1

Shahararren mawakin nan Dauda Kahutu Rarara ya ce, ba da gaske honorable Sha’aban Sharada yake takarar gwamna ba shi ya ajiye tafiyar sa ya koma ta Gawuna.

Mawakin yace duk da shi ne ya tsayar da Sha’aban Ibrahim Sharaɗa takarar Gwamna, amma daga bisani ya gano ta wasa ce.

Rarara ya bayyana hakan ne a hira da Jaridar Intanet ta DCL Hausa suka yi dashi, inda ya zargi Sha’aban da shinshinar PDP a zaɓen Shugaban ƙasa da ya gabata maimakon APC da suka yi yarjejeniya.

” Ni na tsayar da Sha’aban takarar gwamnan da yake yi, ya zo ya same ni yace yana so yayi takarar gwamnan Kano kuma gashi duk jam’iyyun sun tsayar da yan takara, ni da wasu mutane da ba sai na fadi sunansu mu muka je muka Nemo masa jam’iyyar ADP domin yayi takara a cikin ta, don haka duk wata maganar takarar Sha’aban ni nasan ta Kuma na bar shi ne saboda na fahimci ba takarar gaske yake ba”. Inji Rarara

” A cikin Mutane dubu daya da suke tare da Sha’aban dari bakwai ni na kawo su ko kuma wadanda na kawo su suka kawo su, don haka ni na tsayar da shi takarar Kuma na bar shi ne saboda na fahimci ba takarar gaske yake ba “.

A cikin hirar Rarara ya bayyana cewa Nasiru Gawuna yafi kowanne dan takarar gwamnan kano cancanta Saboda nagartar da yake da ita da Kuma yadda ya mika lamarin takarar sa ga Allah

KADAURA 24

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *