Labarai
Bayern ta kori Oliver Kahn, mintuna kalilan bayan lashe gasar Bundesliga

Kungiyar Bayern Munich ta kori shugaban hukumar gudanarwarta Oliver Kahn da kuma daraktan wasanni Hasan Salihamidzic.
Munich ta dauki matakin ne mintuna kalilan bayan ta lashe kofin gasar Bundesliga ta kasar Jamus a ranar Asabar din da ta gabata.
Bayern ta lashe gasar ta bana ne, bayan samun nasarar doke kungiyar Cologne da kwallaye 2-1, abinda ya ba ta damar kammala kakar wasan ta bana da mafi yawan kwallaye a Jamus, domin kuwa makinsu guda da Borussia Dortmund, wato 71.
Yayin wasannin na ranar Asabar Dortmund na neman nasara ne a karawarta ta Mainz amma hakan ba ta samu ba, abinda ya sanya ta rasa damar lashe kofin bana.
Cikin sanarwar da ta fitar, kungiyar ta bayyana Jan-Christian Dreesen a matsayin wanda ya maye gurbin Kahn nan take.
Bayern Munich ta ce sallamar Oliver Kahn ba abun ne mai sauki a gare ta ba, sai dai matakin ya zama dole, domin sabunta tsarin shugabancinta.