Labarai
Da Dumi Dumi- Kotu ta ayyana Musa Iliyasu Kwankwaso a Matsayin Dan Majalisar Kura,Madobi, Garunmala

Kotun sauraron kararrakin zaben Majalisar Tarayya Dana jiha a Kano ta bayyana Dan takarar jam’iyyar APC Musa Iliyasu Kwankwaso a Matsayin Wanda ya kashe zaben Kura Madobi da Garunmalam
Kotun ta bayyana Hakan ne bayan soke nasarar da hon Yusuf Umar Datti na jam’iyyar NNPP saboda Bai ajiye aiki da Jami’ar Bayero ba kwanaki 30 kafin zaben da ya gabata.
Mai shari’a Ngozi Flora Azinge a saboda haka ta umarci hukumar zabe ta kasa INEC ta Yi watsi da takardar cin zaben da ta bashi