Connect with us

Labarai

Dakarun MNJTF sun kashe mayakan ISWAP fiye da 100 a Tafkin Chadi

Published

on

MNJFT july2020 0

Sojojin hadakar da ke karkashin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF daga Najeriya da Nijar da kuma Kamaru sun samu nasarar kashe mayakan ISWAP fiye da 100, cikinsu har da manyan kwamandoji 10, a cikin ‘yan makwannin da suka gabata, yayin hare-hare ta sama da ta kasa a yankin tafkin Chadi.

Kakakin rundunar sojin hadin gwiwar ta kasa da kasa, Kanar Muhd Dole, ya ce dakarunsu da suka kutsa cikin yankunan da masu tayar da kayar bayan ke iko da su a yankin tafkin na Chadi, sun samu nasarar kwace makamai masu yawan gaske, da kayayyakin abinci da kuma miyagun kwayoyi.

Kanar Dole ya kara da cewar, sojoji 18 ne suka samu raunuka yayin artabu da mayakan na ISWAP wadanda suka binne bama-bamai a gefe hanya, sai dai kanar din bai yi karin bayanikan ko an samu wasu dakarun da suka rasa rayukansu ba.

Mayakan Boko Haram da na kungiyar ISWAP da suka balle sun shafe fiye da shekaru goma suna fafatawa da sojojin Najeriya a yankin arewa maso gabashin kasar, rikicin da ya bazu zuwa cikin makwaftanta wato Nijar, Kamaru da Chadi.

Dubban mutane ne dai suka rasa rayukansu, wasu miliyoyikuma suka zama ‘yan gudun hijira, a dalilin tashin hankalin da ake cigaba da yi.

Cikin makon jiya Amurka ta amince da ta saidawa Najeriya jiragen yaki masu saukar ungula gami da wasu makamai na kusan dala biliyan daya domin yaki da ta’addanci.

 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *