Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano Ta Gaza Tabuka Komai A Kwanaki 100 Sai Farfaganda–Musa Iliyasu Kwankwaso

Published

on

IMG 20230913 122046 924

Dan Majalisar Tarayya Mai wakiltar Kura, Madobi da Garunmalam da kotu ta ayyana, Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso, yace addu’ar da suka Yi bayan an zalunce su shi ne dalilin nasarar da suka Samu a gaban kotu, Inda yace basa Yana yada farfaganda a shafukan sada zumunta.

Honorable Musa Iliyasu Kwankwaso ya kuma ce shi ba gwani ne a wadannan shafukan Zamani ba, balle ya yiwa bangaren Shari’a katsalandan a shafukan.

Ya ce shi baya tsoron su kaishi kotu domin Yana da hujjojin da zai gabatarwa shari’a, domin sune suka sami a zaben Kuma a gaban kotu ma basa shakka.

‘Alkwlai sun San me suke, suna da Ilimi kuma ma ai ba Musa Iliyasu Kwankwaso ne ke Shari’ar ba, Allah dai Ya Kai mu Yanke hukuncin gwamna ai za a gani”

Ya ce Inda mutum ya yi laifi ai laifin Yana nan, saboda haka tunda Alkalai suka Yanke wancan hukunci a Shari’ar sa ta Majalisar ai suna da hujjoji na daka suka Yanke ba.

A dangane da cikar gwamnatin NNPP ta Abba Kabir Yusuf kwanaki 100 a kan mulki kuwa, honorable Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce Babu Wani Aiki da Gwamnatin ta yi na Azo a gani.

”Wannan ma ta Sanya shi gwamna Bai Bude aiki ko Daya ba, suka kira Yan Jarida aka Tara a Mambayya yace zai zo amma Bai zo ba, aka saka ana yadawa Kai tsaye a Radio ana fadawa mutane abinda Babu”

Yace ai kamata ya yi a ganshi Yana Bude ayyuka a wurare daban-daban tunda ya kwana 100 a kan mulki.

Iliyasu Kwankwaso ya kuma zargi gwamnatin ta NNPP da shirya farfaganda domin zagaya gari suna yiwa gwamna kirari saboda sun ga an kusa Yanke hukuncin Shari’ar da ake yi ta gwamna

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *