Labarai
DAREN 27 GA RAMADAN: Ya Kamata Mu Zage Damtse-Sheikh Ali Ɗan Abba

A daren yau zamu shiga daren 27 ga Ramadan, daga zancen magabata na ƙwarai sun tabbatar da a irin wannan ranar ake yin gamon dakatar da daren daraja. Kamar yanda yazo a faɗar su Ubayyu Bin Ka’ab da Abdullahi Dan Abbas da sauransu.
Wanda duk ya yi tsayuwar wannan daren yana mai imani da neman lada, to, an gafarta masa abin da ya gabata na daga zunubansa.
Kada a manta da yin addu’ar da Manzon Allah SAW ya bawa Uwar Muminai A’ishah [RA]:
Ita ce …
Allahumma innaka afuwun, tuhibbul afwu, fa’afu anni.
Ma’ana …
Allah kai mai afuwa ne, kana son afuwa, kayi mini afuwa.
Ita wannan addu’ar Malamai sun ce ta ƙunshi dukkan wata buƙata ta duniya da lahira. Tana ƙunshe da addu’oi masu dunƙulallun ma’anoni.
Addu’a a irin wannan rana tana karɓuwa, matuƙar ba ta saɓon Allah bace ko yin shishshigi. Musamman ga waɗanda suka harari lokaci mai tsada, daga ukun dare zuwa fitowar alfijir.
Ya Allah kasa muna da rabon ganin shi da kuma samun rabon da yake zuwa da shi.
Sheikh Ali Dan Abba.
Madogara
Jaridar Zuma Hausa