Labarai
Fatan Mu Kungiyar Ecowas ta kawo karshen matsalar Nijar da Najeriya==Aminu Kurawa

Daga Rabiu Sanusi
An buqaci Qungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika da akafi sa ni da(ECOWAS) qarqashin shugabancin Shugaba Bola Ahmad Tinubu da su duba yiwuwar kawo qarshen matsalolin da ke faruwa a qasar Nijar da sauran qasashen dake maqwabtaka da ita.
Shugaban gamayyar matsakaita da qananan Qungiyoyin Masana’antu na jihar Kano Alhaji Aminu Ibrahim Kurawa ne ya bayyana haka a wata zantawa da wakilin mu ranar Talatar nan.
Alh.Aminu Kurawa yace ya zuwa yanzu da Fara samun matsalar Qasar Nijar da Najeriya dama wasu sauran qasashen ya kawo koma baya matuka wajen cigaban tattalin arziki da ka iya durqusar da kasuwan ci a nahiyar Afrika.
Shugaban Qungiyar yace duba da abokan Kasuwancin su dake kasuwa a tsakanin arewacin kasar nan da kasar ta Nijar wanda ya zuwa yanzu kasuwancin ya zama koma baya idan akai duba da irin kuncin da ake ciki bayan cire tallafin manfetur wannan batu ma ya Daya daga cikin abin da ya ke cigaba da bada gudunmuwar ta matsin Rayuwa.
Kurawa ya qara da cewa yadda wannan Matsala ta kaiga ta taba kananan Masana’antu ya kamata ace gwamnati najeriya tayi wani duba da kyau wajen hadaka da Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika dan kawo karshen wannan tata burza.
“Wannan lamarin ya kawo kuncin rayuwa da ake ciki yanzu,tare da kuntata ga tattalin arzikin da aka shiga yanzu,fatan mu Allah ya maido tunanin shugabanin mu.”
Shugaban na NASSI ya Kuma bukaci gwamnati jihar Kano qarqashin shugabancin Injiniya Abba Kabir Yusuf da ta roka ma su shugaban Qasar Najeriya wajen zaman sulhuntawa da qasar Nijar da kawo saukin wahalar da ake ciki.
Qarshe Aminu Kurawa ya Kuma kara mika kokon barar su ga Mai girma gwamna Abba Kabir wajen taimakawa kamar yadda suka tattauna Kan samawa matasa mafita a jihar Kano.