Connect with us

Labarai

Fatan mu ubangiji yaba Engr Abba Kabir damar yima Al’ummar jihar Kano aiki kamar yadda ya kudurta==Alh,Tijjani Makwarari

Published

on

IMG 20230609 WA01401

Daga RABI’U SANUSI

An bayyana kudurin tabbatar ma da al’ummar jihar Kano samun cigaba a gwamnatin mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf a wannan lokaci da Allah ya bashi nasarar damar zama gwamnan jihar Kano.

Wannan na zuwa ne daga bakin kwamandan Askarawan Kwankwassiya na jihar Kano Alhaji Tijjani Makwarari a wata zantawa da manema labarai da yayi ranar juma’ar nan.

Makwarari yace wannan tafiya tasu tasamo asali ne tun lokaci mai tsayi a baya tare da Shugabanin darikar Kwankwassiya na kasa Engr Rabiu Musa Kwankwaso ba dan komi ba sai dan irin kishin da yake ma al’umma.

Dan Halaliyar Kwankwassiyar kamar yadda ake masa lakabi yace mai girma Jagoran NNPP ya umarce su ne dasu marama Engr, Abba Kabir Yusuf baya a lokacin yawon yada manufar sa na kamfe a kaf fadin kananan hukumomi 44 na jihar Kano,kuma sun tabbatar da hakan ya yuwu.

“Mu Askarawan Kwankwassiya Jajirtattune kuma mu muka tsare akwatunan zabe a kowace rumfar zabe a kona na jihar Kano dan magance matsalolin da ka iya faruwa.”

Shugaban askarawan ya kara da cewa suna matukar godiya bisa yadda aka dauke su da mahimmanci a tafiya mai girma gwamna Abba K. Yusuf tare da cika umarnin Dr. Rabiu Musa Kwankwaso wajen tafiya da su.

“Askarawan Kwankwassiya a lokacin baya mun samu damar karbar horo na aiki daga wajen sojojin dake Bukabu barak da bataliyar Jan guza dan samun horo da Jajircewa a filin horas da masu bautar kasa na karamar hukumar Karaye.”

Sannan Makwarari yace akwai ba’askaren da yayi sanadiyar samun nasarar mai gidan sa da ya fito takara a karamar hukumar kibiya da har sai da akaje kotu Allah ya basu nasara dan Jajircewa.

Kwamandan Askarawan yakuma bukaci duk wanda Allah ya bashi matsayi a wannan tafiya to ya tsaya tare da yima al’umma hidima dan abinda wannan tafiya take bukata kenan.

Daga karshe yace amadadin sa da sauran askarawan Kwankwassiya na jihar Kano suna matukar godiya tare da taya engr Abba Kabir Yusuf da Mataimakin sa Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo da daukacin yan majalisar tarayya da na jiha samun nasara tare da fatan Allah ya basu ikon sauke nauyin da yake Kan su.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *