Connect with us

Labarai

Gwamna Radda ya Sha Alwashin shawo kan matsalar karancin ruwan dake addabar jihar

Published

on

IMG 20230716 WA0031

Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda ta yi fatar daukar matakan da suka dace don magance matsalolin da al’umma ke fuskanta ta dalilin karancin ruwan sha a wasu sassan jihar.

Bayanin hakan ya fito ne bayan wata ganawa ta musamman tsakanin mataimakin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Katsina Alh Mukhtar Saulawa da Manajan Daraktan hukumar samar da ruwan sha ta jihar Engr Tukur Tingilin da kuma hukumar gudanarwar kamfanin samar da hasken lantarki na KEDCO da ya gudana a ranar Laraba 12th Juli, 2023.

Mataimakin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Alhaji Mukhtar Saulawa ya ce an kira taron ne domin tattauna irin matsalolin da ake fuskanta a kananan cibiyoyin samar da ruwan sha na Ajiwa, Daura, Jibia, Malumfashi, da Zobe a Dutsinma. Ya ce ba a hada wasu daga cikin cibiyoyin samar da ruwan da babban layin samar da lantarki na kasa ba, a yayin da wasu ke fama da karancin lantarkin da za su iya amfani dashi don harbo ruwan.

Alh Mukhtar Saulawa ya ce gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda ya ce a shirye take ta ga duk ta magance wadannan matsaloli domin ruwan sha ya wadaci lungu da sako na jihar. Ya kara da cewa gwamnati ta samar da duk abin da ake bukata na harba ruwa a madatsar ruwa ta Ajiwa da sauran wurare domin dai ruwan ya wadata.

Ya ba dukkanin masu ruwa da tsaki tabbacin goyon bayan gwamnatin jiha wajen ganin an samar da isasshe kuma wadataccen ruwan sha a birane da karkarar jihar Katsina.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *