Labarai
Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi ya nada Bala Ibrahim Sakataren gwamnati

Daga Aisha Muhammad
Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Umar Namadi ya nada malam Bala Ibrahim Mamser, a matsayin sabon Sakataren gwamnatin Jihar.
Wannan na cikin wata sanarwar mai dauke da sa hannun Shugaban maiakatan Jihar Alhaji Husaini Ali Kila.
Ta cikin sanarwar, nadin zai fara aiki nan take.
Kafin nadin na shi, Alhaji Mamser tsohon kwamishinan yada labarai da matasa ne na Jihar Jigawa.
Ka zalika gwamnan ya Kuma nada sanata Mustapha Makama Kiyawa a matsayin Shugaban ma’aikatan Gwamnatin Jihar.
Sai Alhaji Adamu Muhammad Garun Gabas a matsayin Shugaban makarantu masu zaman kansu na jihar.
Sauran nade-naden sun hada da Abdullahi S.G Shehu a matasyin babban akantan na JIhar sai kuma Dr. Habib Muhammad Ubale.
Magatakardan Kazaure, Musa A. Kazaure
June 1, 2023 at 8:04 pm
Wannan labarin ya chakude! Bala Mamser shine sabon Sakataren Gwamnatin Jiha.