Connect with us

Labarai

Gwamnan jihar kano Engr, Abba Kabir Yusuf ya yada tsohon shugaban TETFUND a Matsayin sakataren gwamnati

Published

on

IMG 20230530 WA0008

Daga RABI’U SANUSI Kano

 

Sabon gwamnan jihar Kano da ya karbi rantsuwar kama aiki a ranar litinin din nan ya fara gabatar da nadin mukamai na mataimakan da zasu taimaka masa a gwamnatin sa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fara nadin ne da sakataren gwamnati jiha da Dr Baffa Bichi ya zama sabon sakataren gwamnati jihar kano,sai Hon Shehu Wada Sagagi a matsayin Shugaban ma’aikata.

Sauran mukaman sun hadar da Dr Farouq Kurawa a matsayin PPS,sai Hon Abdullahi Ibrahim Rogo dake da mukamin Shugaban tsare-tsare watau chief protocol , yayin da Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa yake matsayin Sakataren yada labaran gwamnan a yanzu.

Wannan bayanin na dauke ne a wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan na jihar Kano ya fitar ga manena labarai a daren ranar litinin dauke da sa hannun sa.

Kazalika sanarwar tace dukkan wadanda aka ba mukaman sun kasance a matakin cancanta da kwarewa tare da irin gudunmuwar da suke badawa wajen ganin jihar Kano taci gaba.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *