Connect with us

Labarai

Gwamnan Jihar Kano ya rushe shugabanin hukumar alhazai tare da nada sababi

Published

on

IMG 20230530 WA0027

Daga RABI’U SANUSI Kano

 

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya rushe shugabancin hukumar Alhazai dake jihar,inda nan take ya maye gurbin wadanda aka sauke da wasu dan tabbatar da anyi hajjin bana mai inganci.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na mai girma gwamna Abba Gida-Gidan Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a daren ranar talatar nan jim kadan bayan tabbatar da rantsar da gwamnan.

Sanarwa tace wadanda sabon gwamnan na jihar ya nada matsayin wadanda zasu shugabanci hukumar sun hada da Alhaji Yusuf Lawan matsayin ciyaman, sai babban sakataren hukumar watau Alhaji Laminu Rabi’u.

Sauran mambobin hukumar sune shiek Shehi Shehi Maihula a matsayin Mamba,Ambasada Munir Lawan,Shiek Isma’il Mangu tare da Hajiya Aishatu Munir Matawalle,sai Dr. Sani Ashir shima matsayin Mamba.

Daga karshe sanarwar tace wadanda aka bayyanar zasu yi gaggawar karbar hukumar ta alhazan daga tsofaffin shugabanin dan tabbatar da gudanar da aikin hajji cikin nasara.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *