Connect with us

Labarai

Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya yi sababbin nade-nade

Published

on

images 8 1

Aisha Muhammad, Kano

 

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal Dare ya nada Alhaji Abubakar Nakwada a matsayun Shugaban ma’aikatan Gwamnatin Jihar.

Wannna na cikin wata sanarwar Mai dauke da sa hannun mataimakinsa na musammam kan kafafen yada labarai Sulaiman Bala Idris

Ta cikin sanarwar nadin zai fara aiki nan take bisa tsarin kundin kasa.

Har ila yau, Dauda Lawal Dare ya kuma.nada Sharifudden F. Jatto a matsayin babban sakatare ga gwamnan sai Kuma Aminu Almajir a matsayin mataimakin Shugaban ma’aikatan Gwamnatin Jihar .

Sauran sune Nura Almajir a matsayin babban mataimakin na musammam kan harkokin siyasa sai Zahradeen Bello Imam da Pharm. Abdulmajid Anka, a matsayin babban mataimaki na musammam kan harkokin ofishin gwamna sai Mustapha Jafaru Kaura, a mtayin mataimaki na musammam kan harkokin kafafen yada labarai.

Sauran sune, Faruk Ahmad Shettiman sai Kabiru Lawal da Muhammad da Shamsuddeen Ibrahim da Ali Akilu Bungudu da Mugira Yusufbsai Kuma Babangida Bisu

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *