Connect with us

Labarai

Hajjin Bana: NAHCON Ta yi karin kudin kujeru

Published

on

images 6

Kujerun Hajji/bana

Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya NAHCON ta sanar da karin naira miliyan Daya da dubu dari tara da Sha 18 kan kudaden aikin hajji da aka sanar a baya.

Kazakika, hukumar ta sanya ranar 28 ga watan da muke ciki na Maris matsayin ranar karshe da maniyyata zasu cika kudin.

Wannan bayani na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar Fatima Sanda Usara.

Fatima ta ce wannan ya zama wajibi la’akari da yadda darajar Nairar Najeriya ke zubewa a kowacce rana.

Hukumar ta bukaci maniyyatan da ke son sauke farali a bana kuma suka riga da bayar da kudin ajiya, su gaggauta cika kudin daga yanzu zuwa 28 ga Maris din nan.

A baya dai hukumar ta tsayar da naira miliyan 4 da dubu dari 5 a matsayin kudin aikin hajjin, kafin daga bisani ta kara naira dubu dari 4, ya zama naira miliyan hudu da dubu 9, sai kuma yanzu da ta sanar da karin kusan naira miliyan biyu.

Idan har wannan kari ya tabbata a yanzu, farashin kujerar aikin hajji zai tashi kan Naira miliyan 6 da dubu dari 9.

Idan dai ba a manta ba, a watan Fabarairun da ya gabata ne hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya ta kayyade kusan naira miliyan biyar a matsayin kudin kuejrar hajjin bana.

Sai dai tun bayan lokacin, hukumar ta soma tababar kara wa maniyyatan kudi bisa dalilan faduwar darajar naira

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *