Connect with us

Labarai

Hukuncin Kotu: Magoya Bayan Mu Masu Da’a Ne Da Bin Doka–Hon Kwankwaso

Published

on

images 9

Tsohon kwamishinan raya karkara na jihar Kano Musa Iliyasu Kwankwaso ya bada tabbacin cewar magoya bayan jam’iyyar APC masu da’a ne da bin doka a kowanne irin yanayi.

Musa Iliyasu Kwankwaso yace har yanzu suna kan fatan samun nasara a Shari’ar da za a Yanke hukunci gobe Juma’a a kotun daukaka Kara.

Yace kafatanin ‘yayan jam’iyyar sun yarda cewar Allah shi ne Mai Bada mulki, Kuma sun fadawa duniya cewar suna da fatan yin nasara a kotun baya, Kuma Allah Ya ba su

Kwankwaso yace shi mutum ne da ya ke kauna zaman lafiya, Kuma ya nuna a aikace lokacin da Bai Sami nasara ba a kotun daukaka Kara kan takarar Dan Majalisar Tarayya da ya yi.

Ya zargi jagororin gwamnatin Kano da koyawa magoya bayan su tayar da tarzoma, Inda yace Nan gaba zasu Yi nadamar abubuwan da suke fada.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya Kuma jinjinawa kotun daukaka Kara bisa yadda ta Yanke hukunci kan zaben gwamnan Zamfara Inda ta Bada umarnin sake zabe a wasu kananan hukumomi

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *