Connect with us

Labarai

Jami’an tsaron Somalia sun dakile yunkurin sake kai harin ta’addanci

Published

on

Sojojin Somalia

Jami’an tsaro a Somaliya sun dakile wani hari da aka yi yunkurin kaiwa kan wani sansanin soji da ke arewa maso gabashin jihar Puntland, inda kuma suka samu nasarar kashe mayakan kungiyar Al-Shabaab 12.

Wasu majiyoyi sun ce sojoji uku na rundunar dakarun tsaron Puntland sun mutu a harin da aka kai sansanin sojojin da ke kusa da kauyen Af-Urur, da sanyin safiyar ranar Lahadi.

A baya-bayan nan kungiyar Al-Shabab ta kaddamar da hare-hare kan jami’an gwamnati da wakilan zabe da kuma fararen hula a fadin kasar, a wani mataki na kawo cikas ga shirin zaben da ake gudanarwa.

A ranar Larabar da ta gabata, kungiyar ta Al-Shabaab ta kai daya daga cikin munanan hare-hare a Mogadishu babban birnin kasar, da kuma fadar shugaban kasa a yankin tsakiyar birnin Beledweyne, inda aka kashe mutane 50 tare da jikkata wasu fiye da 100.

 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *