Connect with us

Labarai

Kazamin fadan Sudan ya jefa rabin ‘yan kasar cikin kunci

Published

on

VDRQK4EHONLZNPJZJOEGGJ6TNA scaled

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da rabin al’ummar kasar Sudan suna cikin tsananin bukatar agajin gaggawa da kuma kariyar rayukansu, biyo bayan kazancewar fada a birnin Khartoum, inda ake cigaba da fafatawa tsakanin sojojin gwamnati da dakarun musamman na rundunar RSF.

Rahotanni sun ce fararen hula na cikin dimuwa gami da laluben inda zasu samu mafaka daga ruwan wutar da jiragen yakin sojojin gwamnati masu biyayya ga shugaba Abdel Fattah al-Burhan ke yi kan dakarun RSF masu goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasar ta Sudan Muhammed Hamdan Daglo, wadanda su kuma suke mayar da martani da manyan bindigogin kakkabo jiragen saman.

Wasu mazauna birnin Khartoum sun ce tuni suka rasa wutar lantarki, yayin da abinci da ruwan sha suka yi karanci matuka, sakamakon kazamin fadan da ya shiga mako na biyar ana gwabza shi, duk da kokarin hukumomin kasa da kasa wajen kulla yarjejeniyar tsagaita wuta.

A baya bayan nan ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya OCHA da ke birnnin Geneva, ya ce a halin yanzu, mutane akalla miliyan 25 ko sama  da haka ke bukatar agajin gaggawa a Sudan, sabanin mutane miliyan 15 da ke halin kunci a kasar, kafin barkewar rikici kan neman mamaye madafun iko a ranar 15 ga watan Afrilun da ya gabata.

Kididdiga ta nuna cewar, rikcin na Sudan ya raba mutane kimanin miliyan guda da muhallansu, daga cikinsu kuma dubu 220,000 sun tsere zuwa kasashe makwafta.

Har yanzu dai yunkurin da Amurka da Saudiya ke yi na kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan din bai samu nasaraba.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *