Connect with us

Labarai

Kotun Musulunci Ta Tasa Keyar Wasu ‘Yan Daudu Zuwa Gidan Gyaran Hali Tare Da Bulala Goma-Goma

Published

on

IMG 20231031 WA0062

Kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a hukumar Hisbah ta jahar Kano ta yankewa, wasu yan Daudu hukunci, bayan sun yi shigar mata dan yin rawar karya kwankwaso a wajen bikin uban gidansu.

Kotun karkashin jagorancin mai shari’a Mallam Sani Tamim Sani Hausawa, ta samu matasan yan Daudun da laifin bayan an karanto musu kunshin tuhumar da ake yi musu, inda nan ta ke suka amsa , sai dai sun roki kotun ta yi musu sassauci.

Mai shari’ar ya yanke musu hukuncin daurin watanni uku ko zabin biyan tarar naira dubu goma-goma kowannen su, tare da yi musu Bulala goma-goma.

Mukaddashin kwamandan hukumar Hisbah na jahar Dr. Mujahiddin Aminuddin Abubakar , ya bayyana cewa hukumar ba zata gajiya ba , wajen dakile aiyukan Badala , domin aikin hukumar shi ne ,yin hani da aikata mummuna tare da kiran aikata kyakkyawa.

Special Reporter to the executive governor of kano state on Hisbah Board
Bashir Muhammad Ahmad

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *