Connect with us

Labarai

Kotun Tarayya Ta Bukaci Wani Lauya Ya Gabatar Mata Wanda Yake Karewa Ranar 6 Ga watan Gobe

Published

on

Alibert Furniture

Babbar kotun tarayya mai lamba biyu dake zaman ta a jihar Kano unguwar Gyadi-gyadi ta gargadi wani lauya mai suna Yahaya Isah Abdurrashid dake aiki a chanbar Dikko and Mahmud da ofishin su ke Dorawa road a unguwar Nassarawa GRA kan ya gabatar da wanda yake karewa a gaban ta a ranar 6 ga watan Disamba mai kamawa na wannnan shekarar ta 2023 da muke ciki.

Tun da fari dai babban sifeton’yan sandan kasar nan Kayode Egbetukun ne ya yi karar wani Dan kasar Labanon Mai suna Maged Ali Taan tare da wani dan kasar nan Mustafa Tiamiyu a kotun da tuhumar hada kai wajan aikata laifi tare da cinnawa wani gida mai lamba 5C dake kan titin Murtala Muhammad a nan Kano wuta. Tin a shekarar 2021.

An dai zargi sun cinnawa gidan wuta ne saboda kwadayjn za su karbi makudan kudaden inshora kafin ‘yan sanda su ta da ballin su. Bayan kuma haya suka kama gidan. A wajan Mai shi.

Tun kuma suna wajan ‘Yan sanda ne lauyan ya karbe su beli, a zaman kotun na wannnan Rana Dan kasar wajan bai hallacci kotun ba kuma koda aka tambayi lauya Yahaya sai ya ce ai bashi a karon farko sai ya ce ai bashi da lafiya ne daga bisani Kuma ya ce ai tsoron zuwa kotun yake.

A nan kotun ta ja hankalin sa kan sani cewa fa shi lauya ne. Masanin doka dan Haka aka daga zuwa ranar 6 ga watan Disamba mai kamawa na wannnan shekarar ta 2023.

Bayan fitowa daga kotun mun so jin ta bakin lauya Yahaya Isah amma yaki cewa komai haka shima lauyan ‘yan sandan Abdussalam Dan mai daki bai magantu ba.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *