Connect with us

Featured

Kungiyar Majma’u Ahbabu Sheikh Nyas ta yi kira ga Tijjanawa su Zabi Abba Kabir Yusuf a Matsayin Gwamnan Kano

Published

on

IMG 20230315 WA0173

Kungiyar Majma’u Ahbabu Sheikh Ibrahim Nyas ta kasa karkashin Darikar Tijjaniyya ta yi kira ga mambobin ta a fadin jihar Kano su zabi Dan Takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar NNPP Abba Kabir Yusuf a zaben ranar Asabar Mai zuwa

Shugaban kungiyar Sheikh Tijjani Shiekh Sani Auwalu Wanda jika ne ga Sheikh Ibrahim Nyas shi ne ya yi wannan kiran yau a Wani Taron manema labarai a sakatariyar ‘yan Jaridu ta jihar Kano.

Yace sun yanke shawarar daukar wannan mataki bayan dogon nazari da suka Yi kan nagartar Dan Takarar gwamnan na NNPP Abba Kabir Yusuf kuma suka ga cancantar sa.

Sun ce suna da kyamkyawan fatan cewar Abba Gida-gida zai Yi aikin kare martabar ilimi, kasancewar shi ne abinda su ka fi bawa muhimmanci.

”’ Ina kira ga ‘yan uwana ‘yan Darikar Tijjaniyya da su fito mazan su da matan su za I injiniya Abba Kabir Yusuf a ranar Asabar domin ya zama gwamnan Kano”

Sheikh Tijjani Shiekh Sani Auwalu ya kuma nesanta ‘yan Darikar Tijjaniyya da wasu da suke amfani sa sunan su suna nuna goyon baya ga Wani Dan Takarar na daban.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *