Labarai
Kungiyar Matasa Ta Kibiya Youth Concern Ta Karrama Kwamishinan Kasa Da Safiyo Na Kano

Kungiyar matasa masu kishin ci gaban Kibiya da ake kira Kibiya Youth Concern ta shirya taro na musamman domin karrama Dan ta Alhaji Adamu Aliyu Kibiya bisa nada shi kwamishinan kasa da safiyo na jihar Kano.
Taron Wanda aka gudanar a garin na Kibiya ranar Lahadi, ya Sami halartar manyan kusoshin gwamnatin Kano da ‘yan majalissu na jiha Dana Tarayya domin nuna girmamawa ga kwamishinan na kasa.
Kungiyar matasan ta Kibiya wadda ta kunshi kowanne bangaren na akidun siyasa, tace an shirya Taron ne domin girmama Alhaji Adamu Aliyu bisa wannan babban mataki da ya hau, kasancewarsa Dan su Mai girmama Jama’a da iya mua’amala.
A jawabin sa, shugaban taron Sarkin Kibiya Sanata U K Umar ya kira ga Jama’ar Kibiya da ma jihar Kano Baki Daya, su taimakawa wannan bawan Allah ya sauke nauyin da aka Dora masa.
”Wannan wuri da aka bashi Yana bukatar a taimaka masa, wuri ne babban wuri, saboda haka ba zai yuwu kowa ya Sami abin da yake so ba, duk Wanda ya taimaka masa ya Sani Allah shi ne Mai bayarwa”
Shi ma a nasa jawabin, mataimakin shugaban masu rinjaye na Majalisar dokokin jihar Kano Alhaji Garba Shehu Fammar ya jinjinawa jagoran Kwankwasiyya na Kasa Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da Kuna Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa gwangwaje su da kujerar kwamishinan kasa.
Ya ja hankalin Yan siyasa da sauran al’umma su kasance masu hakuri duk lokacin da ka rasa Wani abu, domin Allah na sane Kamar yadda ya sakawa Adamu Aliyu Kibiya saboda hakurin sa.
Baba Ladan Aliyu Kibiya, shi ne Wanda ya gabatar da jawabi game da rayuwa da halayen Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, Inda ya bayyana shi da mutum Mai hakuri da juriya da kuma jajircewa.
Da yake mayar da jawabi, kwamishinan na kasa da safiyo Adamu Aliyu Kibiya, ya bayyana farin ciki bisa yadda al’umma suka fito domin girmama shi.
Ya jinjinawa jagororin siyasa dana addini a yankin bisa yadda suka tallafawa tafiyar sa da kuma yankin.
Sannan ya yi godiya ta musamman ga Sunusi Sirajo Kwankwaso bisa yadda yake Dora su a turbar koyon siyasa.
Da yake tofa albarcin bakin sa, mashawarcin gwamnan Kano kan harkokin siyasa Sunusi Sirajo Kwankwaso yace Yana daga cikin mutanen da zasu Bada labarin wane ne Adamu Aliyu Kibiya, saboda shi sheda ne kan yadda yake muamalantar Jama’a.
Taron karramawar ya Sami halartar kwamishinan Ilimi Mai Zurfi Dr Yusuf Ibrahim Kofar Mata da na raya karkakara Hamza Safiyanu Kachako da Yan majalissun Kibiya da Bunkure da kuma wakilin Sanatan Kano ta Tsakiya Abdurrahman Kawu Sumaila.
Daga bisani kungiyar matasan ta Kibiya ta shirya wasan kwallon kafa na musamman a Wani bangare na taya kwamishinan murna.