Labarai
Kwamishinan Bibiyar Ayyuka Na Kano Ya Fara Aikin Tattara Alkalima. Ayyukan Da Gwamnatin Baya Ta Ki Kammalawa.

A cigaba da farfado da jihar Kano wajen ayukan cigaba da gwamnati gwamna Engr Abba Kabir Yusuf keyi daga zuwan sa a matsayin gwamnan jihar, musamman wajen ayukan da suka jibanci gina makarantu da sauran harkon raya jihar mai Albarka.
Shima Mai girma Sabon kwamishinan ma’aikatar bibiyar ayuka da nazari ta jihar Kano Hon Namadi Dala ya fara gudanar da zagayen duba wasu daga cikin ayukan tsohon gwamna Kuma tsohon sanatan Kano engr Rabiu Musa Kwankwaso daya faro kuma ba’a kammala ba a lokacin da tsohuwar gwamnati Ganduje ta yi halin ko in kula kan ayukan.
Amma yazuwa yanzu da mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf ya karbi ragama tare da shan alwashin ganin wadancan ayukan da sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fara batare da kammalawaba ga tsohuwar gwamnati da ta shude tayi tare da gabatar da wasu ayukan ma sabbi dan cigaban jihar da al’ummar ta.
Cikin ikon Allah sai gwamnan yayi katari da kwamishina Mai kokarin ganin anyi aikin da ake bukata a wannan ma’aikata ta bibiyar ayuka da nazari watau Hon Namadi Dala wanda kusan mako biyu kenan da rantsar dashi matsayin Shugaba a wannan hukumar bai yi kasa agwuiwa ba dan fara bibiyar dukkan ayukan da ba’a kammala ba kamar yadda mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci kwamishinonin suyi wajen aiki tukuru.
A zagayen da kwamishinan ya gabatar a ranar larabar, ya ce kamar yadda mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf ya basu aiki wajen zagawa dan duba dukkan ayukan da basu kammalu ba tare da bashi rahoto akan hakan dan zaunawa tare da nemo hanyar karasa ayukan.
Hon Namadi ya kuma bayyana cewa yazuwa yanzu zuwan Engr Abba Kabir Yusuf akwai ayukan da yawa akai watsi da su amma ya zauna da Yan kwangilar tare da basu umarnin su ci gaba da aikin su Kuma a halin yanzu suna kan cigaba.
“Kamar yadda muka zagaya daku kunga wadannan makarantu da sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya assasa ba’a kammala ba kuma gwamnati baya bata kula ba dan haka a yanzu zuwan Engr Abba Kabir Yusuf mun dauki damarar cigaba da wannan aiki.”
Kwamishinan ya Kuma tabbatar ma da Jama’a cewa wannan gwamnati bata da burin da ya wuce ganin tayima al’umma aiki kamar yadda tayi alkawarin dan haka bazata ba mutane kunya ba.
Hon Namadi ya kuma tabbatar da cewa ofishin sa zai cigaba da bibiyar dukkan ayukan da yakamata ace an samu tare da ciyar da jihar Kano da kuma Al’ummar gaba musamman yadda Mai girma gwamna Abba Kabir ya ke da wannan niyya da ta samo asali daga Engr Rabiu Musa Kwankwaso na aiki tukuru dan sune al’ummar jihar suke bukata a halin yanzu.
Shugaban ma’aikatar bibiyar ayuka da nazarin yace wannan ofishi nasa a shirye yake wajen ganin an gudanar ma da Jama’a ayuka masu inganci kamar yadda mai girma gwamna ya kudurta.
Wasu daga cikin ayukan da kwamishinan ya ziyarta sun hadar da Kwalejin Lafiya dake kan titin Audu bako watau Magwan da wasu sashe guda ukku a cikin makarantar North West, Gidan Mataimakin Gwamna dake cikin fadar gwamnatin Kano tare da Kwalejoji kere-kere dake kananun hukumomi Rimi da Kumbotso da tsohon sanatan Kano Engr Rabiu Musa Kwankwaso ya assasa a zamanin sa.