Connect with us

Labarai

Kwanaki Dari Na Gwamna Umar Namadi : Sabuwar Jigawa Ta Dau Saiti

Published

on

IMG 20230906 WA0141

Daga Mika’il Tsoho, Dutse

 

Duk da cewar jihar Jigawa ta share kimanin shekaru talatin da biyu da samun jiha, amma haryanzu jihar na jerin wasu jihohin qasar nan dake fama da talauci, yawan yara marasa zuwa makaranta, yawan mutuwar mata masu ciki da qananan Yara.

Haka kuma duk da kasancewar jihar ta sami hazuqan gwamnoni har guda tara, amma akwai sauran rina a kaba duk da irin dumbin arziqin al’umma, masu ilimi da albarkatun qasa a kowanne yanki na jihar baki daya.

Malam Umar Namadi wadda shi ne gwamna na Tara a jerin gwamnonin jihar, cikin kwanaki far da ya share akan karagar mulkin jihar, ya bijiro da kyawawan manufofi wadanda ke nuni da cewa bisa dukkan alamu jihar tayi nasarar jagora kuma jajirtaccen gwamna Mai kishin cigaban jihar ta kowanne fannin rayuwa.

Tun farko dai gwamnan bayan Saba-laya a matsayin gwamna, duk da kasancewarsa tsohon mataimaki gwamnan da ya gabata, ya fara da bibiyar ma’aikatu tareda bibiyar ayyukan da ake gudanarwa domin tabbatar da cewa komai na tafiya bisa qa’ida.

Sannan gwamnan ya kuma nada kwararrun mutane a matsayin Sakataren gwamnati da shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, kwamishinoni, sannan daga bisani masu taimaka Masa na musamman.

Gwamnan ya kuma kafa kwamitoci daban-daban musamman akan matsalar qarancin ma’aikata wadda take barazanar gurgunta aikin gwamnati da harkokin fansho a jihar baki daya.

Haka kuma cikin kwanaki Darin, gwamnan yayi nasarar gudanarda ayyukan cigaba wadda suka hadarda rabawa mata dubu daya naira bilyan guda, yadda kowacce daya ta Sami naira dubu hamsin.

Sannan ya tallafawa manoma da tallafin ragin kudin taki daga naira dubu N28,000 zuwa dubu N16,000, sannan gwamnan ya bayarda zunzurutun kudi har kimanin naira bilyan daya domin sayen motocin noma (tantan) guda 54 domin tallafawa manoma.

Gwamna Namadi a yunkurinsa na ragewa al’ummar jiharsa radadin rayuwa, ya amince da kashe tsabar kudi har kimanin naira bilyan N3.848 domin sayen kayan abinci wadda suka hadarda buhun shinkafa 600 daidai da Tirela 70 da kuma buhun Masara da Gero 600 daidai da Tirela 54 domin rabawa al’umma a qananan hukumomi 27 dake fadin jihar.

Haka kuma duk a cikin kwanaki Darin, gwamnan ya amince da kashe tsabar kudi har kimanin naira milyan N167.024 domin biyan kudin karatun dalibai ‘yan asalin jihar dake karatun digiri a jami’o’in FUD, BUK, KUST da kuma jami’ar UNIMAID.

Harwayau, gwamna Namadi cikin kwanaki Darin ya kuma bibiyar harkar mata, yara da marayu domin ganin an inganta rayuwarsu ta hanyar inganta gidajen marayu, tabbatarwa bawa mata masu ciki da Yara kanana magani kyauta a duk Asibitocin gwamnati fake jihar.

Haka kuma gwamnan ya dukufa wajen ganin an inganta fannin ilimin lafiya dake, Jami’ar jiha ta Sule Lamido dake Kafin Hausa domin cigaba da samarda sabbin likitoci da zasu cike guraban same Asibitocin jihar baki daya.

Dangane da matsalar ambaliyar ruwa kuwa, gwamnan ya nemi qwararrun masana domin ganin an shawo kan matsalar, wadda hakan yasanya gwamnan kashe maqudan kudade wajen sayo manyan motocin yasar kogi, wadda zasu yashe hanyoyin ruwan dake barna a jihar, wadda zuwa yanzu sun yashe kimanin samada kilomita 60 cikin aikin yashe hanyar ruwa daga Ringim zuwa Guri.

Gwamnan ya kuma tallafawa qungiyoyin aikin gayya a jihar da kayan aikin gayya, kwale-kwale da sauran kayan bada tallafin gaggawa gamida Gina ganuwar ruwa a garuruwan dake fama da barazanar ambaliyar ruwa wadda takai kimanin samada kilomita dari a fadin jihar.
Dangane bunqasa kasuwanci da tattalin arziki kuwa, gwamna Namadi ya kafa kwamiti na musamman domin inganta cibiyar kasuwanci kasa-da-kasa dake Maigatari, wadda ya ja hankulan kamfanoni samada 57 wajen ganin sun shigo jihar domin zuba jarinsu.

Haka Kuma gwamnan a yunqurinsa na bunqasa qananan kasuwanci a jihar, ya baiwa masu qananan kasuwanci su kimanin dubu daya jarin naira N150,000 kowanne domin bunqasa kasuwancinsu.

Gwamna Namadi ya kuma Sha alwashin bunqasa kasuwanci da ma’aikatu ta hanyar amfani da fasahar zamani, yadda ya nada mataimaka na musamman domin bunqasa cibiyar Galaxy dake jihar.

Daga qarshe dai gwamnan had kullum Yana cigaba da neman addu’o’in al’ummar jihar da goyon bayansu wajen ganin ya sauke nauyin da Allah ya Dora masa na ciyarda jihar gaba.a

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *