Labarai
Kwankwaso ya zargi gwamnatin NNPP da kokarin batawa gwamnatin Tarayya suna a Kano kan rabon Tallafi

Tsohon Kwamishinan Raya Karkakara Na jihar Kano Kuma Dan takarar Majalisar Tarayya na mazabar Kura Madobi da Garunmalam Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso daman ya gargadi al’umma Kan zaben kwankwasiyya saboda zasu zo da manufar muzgunawa Jama’a.
Honorable Musa Iliyasu Kwankwaso yace dukkan abubuwan sa yayi hasashen zasu faru sun Riga sun faru, amma ya yi gargadin cewar duk wanda Allah Ya bawa dama Kuma ya kuntatawa al’umma Allah ba zai bar shi ba.
”Idan za a iya tunawa tsohon Gwamnan Kano Dr Malam Ibrahim Shekarau ya ja hankalin sabon gwamnan na Kano kan abinda yake Yi, amma aka Yi ca akan sa saboda yace gwamna ya tsaya ya duba nauyin da Allah Ya Dora masa”
Honorable Kwankwaso yace Yana mutukar tausayawa gwamnan na Kano Abba Kabir Yusuf kasancewar ya San Mai gidan sa ba zai bashi dama ya yi aiki ba, Kuma duk abinda yace zasu faru a gwamnatin sun faru.
Yace dukkan abubuwan da ‘yan kwankwasiyya suka ce suna aikata Suma yanzu suna aikata irin sa, Kuma lokaci na zuwa da zasu shelantawa mutanen Kano abinda gwamnatin Kanon keyi.
Yace sun yi zargin cewar an Bada filaye da rumfuna ba bisa kaida ba, Inda yace Suma suna Nan suna Tara Alkaliman bayanai abubuwan Dake faruwa karkashin gwanantin ta NNPP.
”Kace an Gina Daula ba bisa kaida ba, to ai kamata yayi ka kira dukkan Wadanda kake zargin suna da hannu ciki su baka bayanai kafin ka dauki Wani mataki”
Ya Sha Alwashin cewar Nan gaba Kadan zasu fitar da bayanai da suka Tattara kan gwamnatin ta NNPP da irin kwangiloli da suke bayarwa’ da kuma mutanen da ake bawa.
Ya kuma jaddada matsayar su ta dogara ga Allah a Shari’ar da suke Kan zaben gwamnan Kano Inda yace suna da kyakkyawan fatan samun nasarar Gawuna da Garo a Shari’ar.
Yace suna da bayanai Dake nuna cewar Yan kwankwasiyya sun fara tunanin tafiya daukaka Kara da kuma Inda zasu Samo kudin lauyoyi.
Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso ya kuma zargi gwamnatin NNPP da kin raba Tallafin rage radadi da Gwamnatin Tarayya ta bayar domin Bata sunan shugaban kasa, Inda ya Shawarci Shugaba Tinubu ya Rika amfani da shugabancin jam’iyyar APC domin kaiwa ga talakawa.