Connect with us

Labarai

LMC ta bawa Kano pillars damar komawa buga wasa a Sani Abacha Stadium.

Published

on

IMG 20220415 WA0078

Hukumar dake gudanar da gasar firimiya ta kasa wato LMC ta amince da komawar kungiyar Kano pillars gida da buga wasanta a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata, a Kano.

 

Sakataren hukumar ne Alhaji Salisu Abubakar ya sanar da hakan bayan da kungiyar ta Sai Masu Gida ta mikawa hukumar bukatar ta na komawa gida domin cigaba da fafata wasannin ta.

 

Hakan na nufin kungiyar ta Kano pillars zata dawo gida domin cigaba da karbar bakuncin kungiyoyin wasa daban-daban.

 

Kano pillars dai ta shafe tsahon lokaci bata buga wasa a filin wasa na Sani Abacha ba, inda ta koma filin wasa na Ahmadu Bello dake kaduna kafin daga bisani ta koma Katsina filin wasa na Muhammadu Dikko inda take karbar bakuncin wasannin ta.

 

Yanzu haka dai Kano pillars zata fafata da Katsina United a gasar firimiya ta kasa a makon ta muke ciki, bayan kammala shiri tsaf domin buga wasan a filin wasa na Sani Abacha.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *