Connect with us

Labarai

Mu na Maraba Da Madugun Kwankwasiyya zuwa APC -Kwankwaso

Published

on

images 9

Tsohon kwamishinan raya karkara na jihar Kano Kuma Wanda ya yiwa jam’iyyar APC takarar Majalisar wakilai na Kura Madobi da Garun Malam Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce suna maraba da madugun kwankwasiyya sanata Rabiu Musa Kwankwaso da makaraban sa idan yace zai dawo jam’iyyar.

Musa Iliyasu Kwankwaso yace dawowar su APC karuwa ce ga jam’iyyar, a saboda haka kofa a bude ta ke a kowanne lokaci kasancewar a lokutan baya ma, an Yi tafiya tare tsakanin sanata Kwankwaso da Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Sai dai yace dawo jam’iyyar da kuma batun Shari’ar gwamna abubuwa ne daban-daban, kasancewar a farkon wata Mai kamawa ake sa ran Yanke hukunci kan batun.

Yace lauyoyin su da kuma na NNPP suna ta kokarin gabatar da bayanan su gaban kotun koli kafin Yanke hukunci, domin har yanzu ba a San wadanne alkalai ne zasu zauna kan Shari’ar ba.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya Kara da cewa suna sa ran samun nasarar Gawuna da Garo a Shari’ar, Kuma Koda bayan rantsar dasu ne suna iya karbar bakuncin masu dawowa jam’iyyar ta APC, domin tarbar su.

Sai dai yace siyasa ba a haniya da soshiyal media ta ke ba, amma idan sanata Kwankwaso ya janye shawarar sa ta yin hadaka da PDP zai dawo APC suna maraba da shi

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *