Connect with us

Uncategorized

Mun Nemi Hadin Kan Yan Sanda Da Hukumar Yaki Da Cin Hanci Don Kawar Da Almundahana A Ma’aikatar Kasa–Hon. Kibiya

Published

on

IMG 20230905 WA0194 2

Kwamishinan Kasa da Safiyo na jihar Kano Alhaji Adamu Aliyu Kibiya ya lashi takobin Kara bunkasa harkokin ma’aikatar ta hanyar fasahar Zamani da sababbin tsare-tsare.

Kwamishinan ya bayyana Hakan ne lokacin da ya jagoranci shugabannin ma’aikatar a wata ziyara da yake hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano da kuma kwamishinan ‘yan Sandan jihar don neman goyon bayan su kan ayyukan da ya Sanya gaba.

Yace ma’aikatar karkashin kulawar sa ta Samar da sashin binciken kwakwaf na Zamani da a Turance ake kira da forensic unit domin yaki da ayyukan Jabu da almundahana a ma’aikatar.

Alhaji Adamu Aliyu Kibiya ya ce ziyarar hukumomin biyu na da nufin Kara inganta alakar aiki da fahimtar juna, kasancewar gwamnatin Kano karkashin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta kudiri aniyar tsaftace yadda ake hada-hadar kasa a jihar nan.

”Wannan ma’aikata tamu ta kasa da safiyo gida ne na kowa da kowa a jihar Kano saboda muhimmancin kasa a jihar Kano”

Kwamishinan yace Babu yadda ayyukan ma’aikatar zasu tafi daidai ba tare da wadannan hukumomin ba da makamantan su.

Yayin da yake jawabi gaban shugaban hukumar yaki da cin hancin ta jihar Kano, Alhaji Adamu Aliyu Kibiya ya Nemi taimakon hukumar wajen aiki tare don kwato hakkin marasa karfi tare da dakile aikta rashin gaskiya.
Ya kuma kokawa kwamishinan ‘yan Sandan jihar Kano game yadda bincike kan Wani zargi ke samu matsala a lokutan baya, Inda yace Hakan na cikin dalilan ziyarar domin neman taimakon rundunar.

A jawabin da ya gabatar, shugaban hukumar yaki da cin hancin Barista Muhuyi Magaji Rimingado ya bawa Kwamishinan tabbacin goyon baya domin samun nasarar ma’aikatar.

Ya kuma bukaci kwamishinan na kasa da safiyo da ya Samar da tsarin yaki da cin hanci da rashawa a ma’aikatar.

”Hakika a shirye muke nu Yi aiki tare, Ina Mai tabbatar Maka kaso Mafi yawa na korafe-korafen Dake gaban mu na sha’anin kada ne”.

Shi ma a nasa bangaren kwamishinan ‘yan Sandan jihar Kano Hussaini Gumel ya bawa Kwamishinan tabbacin goyon baya domin samun nasarar ayyukan sa , Inda yace a shirye suke koda yaushe su gudanar da ayyukan al’umma.
Ya kuma yabawa ma’aikatar ta kasa bisa yadda ta kirkiro sashin bincike na Zamani domin yaki da ayyukan Jabu da Samar da ingantattun hujoji kan kowanne Batu.

 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *