Connect with us

Labarai

Musa Iliyasu Kwankwaso Ya magantu kan Wani Bidiyon Tsohon Gwamna Ganduje Kan Shari’ar Zaben Gwamna

Published

on

images 9

Tsohon kwamishinan raya karkakara na jihar Kano Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso yace bidiyon sautin da aka saki na tsohon Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje cin amanar abokan Hulda ne da kuma aikin Jarida.

A wata hira da manema labarai bayan Sakin faifan bidiyon, Musa Iliyasu Kwankwaso yace abin Bai daga musu hankali ba, domin yasan ka’idar aikin Jarida ta fadin abin da ya wakana bisa gaskiya.

‘A Matsayina na Wanda ya karanta aikin Jarida ya kamata ace idan dauko labari ka Fadi ma’anar sa, a Ina aka Yi Kuma me aka fada, ka ga Babu! Kawai yace ayi hakuri mun Fadi zabe Kuma ya fada yace ba ayi mana daidai ba.

Yace shi a wurin sa, wannan batun ba shi da alaka da kotun da suka Kai Kara Wanda suka Gabatar da shaidu.

”Kuma abin Jin dadi akwai sheda wadda Dr Aminu Tsanyawa, wadda muka kawo ballot paper aka kirga aka tantance aka tabbatar da cewar wannan kirga da aka Yi mun kada jam’iyyar NNPP da kuri’ a talatin da shida Kuma kotu ta karba”

”Hankalin su ya tashi suka dauki Kara suka Kai appeal a yau Allah Ya taimake mu wannan appeal ta tabbatar da cewar ta Kori wannan appeal din masu, an tabbatar da shedar Dr Aminu Tsanyawa”

Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso ya kuma yi kira ga yayan jam’iyyar APC da su ci gaba da addu’ar neman nasarar Gawuna da Garo a hukuncin da kotu zata Yankee.

Kazalika, Musa Iliyasu Kwankwaso ya kuma zargi NNPP da gwamnatin ta da shirya zanga-zangar da aka ce kungiyoyin fararen hula ne suka shirya domin nuna kyama da yunkurin Bada cin hanci ga kotun sauraron zaben gwamnan Kano.

Yace kwanaki Kadan kafin zanga-zangar, ya fallasa cewar an gudanar da Wani taro a Abuja Inda aka shirya wannan zanga-zangar.

Ya Kuna zargi jam’iyyar ta NNPP da hada wata tawagar masu fada aji domin Kai kukan su ga Shugaba Tinubu

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *