Labarai
NALDA Ta Samarda Makarantun Horas Da Manoma A jihohin Ogun, Katsina, Abia Da Borno

Daga Mika’il Tsoho, Dutse
A yunkurinta na ceto ‘yan Kasa daga kangin yunwa da samarda nagartaccen sakamako ta fuskar aikin gona, hukumar kula da share filayan aikin noma ta kasa (NALDA) ta samarda Makarantun Horaswa ga manoma a jihohin Borno, Abia, Katsina da Ogun.
Wannan na kunshe cikin wata takarda wadda babban jami’in hukumar ta NALDA, Kaka Alhaji Mustapha ya rattabawa hannu tareda mika takardar ga manema labarai.
Yace bayan shirye-shirye daban – daban da hukumar ta NALDA ke gudanarwa ga manoma mata da maza, yanzu kuma hukumar ta kafa makarantar da zata rika baiwa su manoman horo akan dabarun aikin noma yayinda suma wadanda suka sami horon kuma suka kware zasu samu damar horas da wasu domin ganin ankai ga nasara akan irin aiyukan da ita hukumar tasanya agaba.
Haka kuma ya Kara da cewa, samarda makarantun zai taimaka matuka sosai wajan horas da manoma dakuma gudanar da duk wasu shirye-shirye wanda hukumar takeyi cikin sauki musamman wajan baiwa y’an “saa – kai” (volunteer) da sauran manoma bita akan aikin gona cikin sauki.
Jami’in yace, irin aiyukan da hukumar NALDA take aiwatarwa awasu sassa na kasar Nijeriya musamman na katafariyar gona maisuna “Integrated Organic Farm Estate” a Jihar Borno. Ansamar da itane domin kyakkyawan zaton cewa matasa da mata na wannan jihar ta Borno zasu samu ilimi da dubaru na musamman wajen koyon sana’ar aikin gona musamman a bangaren harkar kiwon kaji masu kwai da nama, kiwon kifi, kiwon zuma, kiwon dabbobi na shanu da tumaki. Haka kuma da koyon aikin sarrafa kayan amfanin gona dakuma sayar dasu a kasuwar zamani.
Kaka, yakara dacewa NALDA zata chigaba da iyakacin bakin kokarinta wajen ganin ta chika dukkananin alkawarinta musamman wanda suke gabanta domin chigaban manoma.
Kaka yace Makarantun zasu gudanar da karatu a mataki na farko a makarantar da aka kafa din, za’a farane da takardar shaidar Diploma wato ND abangaran fannin aikin gona, sauran kwasa – kwasan, sun hada da National Diploma (ND) ta kimiyyan aikin gona da kiwo (Agricultural Technology & Animal Production) dakuma Diploma akan kiwon lafiya (Diploma in Health Technology).
Haka zalika, makarantar zata bada horo akan dabarun hannu abangaran aikin gona, kuma an amince da kwalin shaidar karatunsu afadin tarayyar kasarnan batareda nuna bambamchi ba.
Shima jami’in hulda da hukumar kuma masani akan fannin ilimi na KLM & KHALS da yake aiki da hukumar ta NALDA, Mr Samuel Ono yakara da cewa su al’ummar Jihohin Abia , Ogun, Katsina da Borno ne zasufi amfana da alkairin wannan makarantun da hukumar NALDA ta samar a Jihohin nasu.
Yakuma bukaci wadanda shirin zai shafa kaitsaye acikin wadannan wurare dasu rungumi shirin da hannu biyu domin ganin irin muhinmancin da shirin yake kunshe dashi. Yace akalla su dauki nauyin karatun dalibai biyar biyar na iyalansu a duk shekara domin hakan zai taimaka wajan rage zaman banza kuma matasa da dama zasu zama masu dogaro da kansu agaba.