Connect with us

Featured

Nan Gaba Kadan Za’a Kammala Titin Wuju-Wuju Da Kasuwar Kwankwaso ta Zamani–Hon Ibrahim Namadi

Published

on

IMG 20230726 WA0213

Kwamishinan ma’aikatar bibiyar ayuka da nazari na jihar Kano Hon Ibrahim Namadi Dala ya tabbatar da yunkurin gwamnati jihar Kano wajen ganin ta tabbatar da karasa ayukan da ta sa gaba na Titin Wuju-Wuju da Kasuwar Zamani dake Garin Kwankwaso a karamar Hukumar Madobi dama wasu sauran ayukan.

Ibrahim Namadi ya bayyana hakane ga manema labarai a ranar laraba yayin da ya fita rangadin duba ayukan da ba’a karasa ba da aka fara tun lokacin Dr Rabiu Musa Kwankwaso da tsohuwar gwamnati Ganduje ta yi watsi da shi.

Namadi yace babu abun bacin rai da ya samu sai lokacin da ya ziyarci makarantar koyon kere-kere dake karamar hukumar Madobi da yasamu gaba daya makarantar ta lalace sai dai aka samu fara gudanar da jeka kadawo acikin ta.

Kwamishinan yakara da cewa acikin makarantar akwai dalibai (700) amma malaman dake koyarwa ta din-din-din guda(4) ne kacal,sannan an Kuma bi makarantar an kwace wasu daga cikin kayan aikin ta, tare da lalacewar wani sace na ginin ta.

“Yadda muka zagaya Kama daga titin Wuju-Wuju, ofishin mu na dindin din, makarantar koyan aikin lafiya da kasuwar Zamani ta Kwankwaso da sauran guraren da muka kewaya zamu mika rahoto akan abinda muka gani dan daukar mataki.”

Namadi Dala,ya bukaci Yan kwangilar da akaba karasa ayukan nan da su tsaya tsakanin su day Allah wajen gudanar da aikin mai nagarta tare da Jajircewa kamar yadda mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarce su da yi.

Dala ya kuma tabbatar ma da Yan kwangilar cewa su sani Abba Kabir zai bibiya abinda sukayi tare da dubawa,idan yaga sabanin haka to lallai zai iya daukar matakin da ya dace.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *