Labarai
Napoli ta tsuga farashin miliyoyin euro akan Osimhen

Kungiyar Napoli da ke Italiya ta kara farashin dan wasanta na gaba Victor Osimhen, biyo bayan tarihin da ya kafa na taimaka mata wajen lashe kofin gasar Seria A, karo na farko cikin shekaru 33.
Bayanai daga majiyoyi sahihai, sun ce Napoli ta ce a halin yanzu duk wata kungiya da ke neman kulla yarjejeniya da Osimhen dan Najeriya, to fa sai ta ajiye tsabar kudaden da yawansu ya kama daga euro miliyan 150 zuwa 160.
Kafin daukar wannan mataki dai, manyan kungiyoyin kwallon kafar da ke nahiyar Turai ne ke zawarcin dan wasan mai shekaru 24.
Kungiyoyin da ke hankoron neman kulla yarjejeniya da Osimhen sun hada da Chelsea, Bayern Munich, PSG, Arsenal da kuma Manchester United.
Rahotanni sun ce a halin da ake ciki tuni kungiyar Chelsea ta janye aniyar sayen Osimhen daga Italiya, tana mai korafin cewa kudin da Napoli ta lafta masa yayi yawa.
Yanzu haka dai Osimhen dan wasa maf iyawan kwallaye da adadin 23 a gasar Seria A, kuma ya jefa kwallayen ne a jimillar wasanni 27 da ya buga a kakar wasa ta bana.