Connect with us

Labarai

Rahotannin cin zarafin mata sun karu a Sudan

Published

on

CS2FZ34BUVPINOVATTG33HUIAI scaled

Rahotanni da dama da suka bulla a Sudan, sun bayyana yadda dakarun rundunar musamman na RSF ke cin zarafin mata ta hanyar yi musu fyade, lamarin da ya tilastawa masu rajin kare hakkin dan adam da jami’an lafiya, amfani da kafofin sadarwar zamani wajen gargadin wadanda ke cikin hatsarin fuskantar tashin hankalin.

Ya zuwa yanzu dai an samu nasarar yada hujjoji da dama ta kafofin sada zumunta kan zarge-zargen da ake yi wa dakarun RSF na aikata fyaden, duk da cewar kungiyoyin farar hula na fuskantar kalubalen yada bayanan, saboda rashin karfin sadarwar intanet a kasar ta Sudan, inda fadan da ake gawbza wa tsakanin dakarun kai daukin gaggawar da kuma sojojin gwamnati ya shiga mako na biyar.

Abu ne mawuyaci a iya tantance sahihancin rahotannin da ke tuhumar dakarun na RSF kan tafka ta’asar, wadanda wasu bayanai suka ce suna cin zarafin wasu matan ne a gaban iyalansu.

Wasu majiyoyi sun ce da fari mata ‘yan kasashen ketare ne ke fuskantar cin zarafin na fyade, amma daga bisani tashin hankalin ya fadada zuwa kan mata ‘yan asalin Sudan.

Neimat Abubakar Abbas babbar jamai’a a kungiyar SIHA da ke kare hakkin mata a yankin kuryar gabashin Afirka, ta ce suna da tabbas akan rahoton wasu mata akalla 20 da aka yi wa fyade a kudancin birnin Darfur, masifar da tace ta kara yin karfi a Kudancin yankin Darfur, inda ko a watan da ya gabata, sai da aka sace wasu mata akalla 24, tare da yi musu fyade a wani sansanin ‘yan gudun hijira.

 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *