Connect with us

Labarai

Ramadan: Alhaji Aliko Dangote Ya Kudiri Aniyar Tallafawa Mabukata Da Kayan Abinci

Published

on

xScreenshot 20240225 140055.png.pagespeed.ic .oCfrLd95Zf 1

Hamshakin Mai arzikin Nan Alhaji Aliko Dangote Mai son tallafawa alummar kasar nan don saukaka musu daga halin matsin tattakin arzikin da ake ciki zai tallafawa mabukata kayan abinci kyauta don yin azumin watan Ramadan cikin nishadin.

Diyarsa Hajiya Fatima Aliko  Ɗangote   ce ta bayyana hakan, yayin wani taron ganawa da yan Jaridu na Arewacin Najeriya daya gudana a birnin Kano.

Hajia Fatima ta ce mahaifinta ya jima yana gudanar da ayyuka domin kyautata rayuwar alummar jahar Kano, shi yasa a wannan lokaci ya kudiri aniyar tallafawa mabukata da kayan abinci sakamakon halin kunci da matsin rayuwar da ake ciki

Ga wadanda Ke bibiyar ayyukan jinkai na Gidauniyar Dangote suna sane da yadda ake gudanar da ayyukan inganta rayuwar Jama’a a asibitoci baya ga bayar da abinci ga Mabukata tsawon shekaru.

1 Comment

1 Comment

  1. Hassan mamman

    February 29, 2024 at 9:09 am

    Masha Allah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *