Connect with us

Labarai

Rundunar ‘Yan Sandan Kano Tace Dokar Takaita Yawon Adaidaita Na Nan Daram

Published

on

download 5

RABI’U SANUSI a Kano.

Rundunar Yan sandan jihar kano karkashin jagorancin CP Mamman Dauda ta shelantama al’ummar jihar kano musamman musulmai cigaba da samar da isashen tsaro a fadin jihar a lokacin azumi da ma bayan sa.

Wannan na dauke a wata sanarwa da kakakin rundunar SP Abdullahi Kiyawa ya fitar ga manema labarai a ranar laraba wannan makon.

Sanarwar tace kasancewar jihar Kano na gaba a harkokin Kasuwanci a wannan lokaci akwai baki daga ciki da wajen kasar nan, musamman akwai shirye-shiryen gudanar da Karamar sallah dan haka hukumar ta kara daura damarar da tsarin tsaro a jihar dan haka ya yi kira da jama’a dasu kasance masu bin doka.

Haka Kuma sanarwar tace batun dokar masu adaidai ta sahu da hukumar ta sanar kwanan baya tana nan daga karfe 10 zuwa 6 na dare zuwa safiya,inda kuma yace rundunar da sauran jami’an tsaro da sauran jami’an kula da ababen hawa ta Karota zasu cigaba da kama wadanda aka kama ya karya dokar.

“Dokokin sun hadar da dokar masu adaidai ta fara goma na dare zuwa shidda 10-6, sai dokar hana hawan dawakai da sunan kilisa, kazalika dokar hana buha nokout ko bangas ita ma dukkan wanda aka kamashi tare da hukunta shi.

Haka Kuma sanarwar yace masu zuwa masallatai dan gudanar da ibada kamar wa’azi a lokacin wannan wata dole sai an sa kula da masu zuwa da dawowa su zama masu sanar da jami’an tsaro,sannan kuma sun bayyana bin umarni da masu tukin ababen hawa tare da kaucewa tukin ganganci,da kaucewa gudu akan tituna da yake haifar da hadari.

kwamishinan Yan sanda ya kuma roki mutanen jihar kano dasu cigaba da addu’o’in samun zaman lafiya tare da sanar da jami’an tsaro dukkan wani motsi da basu yarda da shi ba ko kuma su sanar da jami’an tsaro ta wannan lambobin 08123821515,09029292926,08032419754.

Daga karshe CP Mamman Dauda da sauran jami’an tsaro suna yima al’ummar jihar kano barka da shigowar watan azumi tare da fatan samun babban rabo.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *