Connect with us

Labarai

Sabon Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi Na Kano Dr Yusuf Kofar Mata Ya Sha Alwashin Bunkasar Bangaren

Published

on

IMG 20230626 WA0210

Kwamishina Ma’aikatar Ilimimai Urfi Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata yace gaskiya da rukon amana da jajircewa sune ginshikin ci gaba.

Kwamishina ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi ragamar tafiyar da Ma’aikatar a yau.

Dr. Kofar Mata ya jaddada cewa gwamnatin Engr. Abba kabir Yusuf ta zo ne domin ta samar da abubuwan kyautata rayuwar jama’a jihar Kano tare da maido da darajar ilimi.

Kwamishina ya bada tabbacin bunkasa ilimi mai zurfi ga matasan jihar nan tare da inganta manyan makaratu malakin gwnatin jihar Kano.

Ya jaddada kudirinsa na tafiya kafada-da-kafada da ma’ikatan Ma’aikata Ilimi Mai Zurfi da kuma manyan makarantun ilimi gami da barin ofishinsa a bude domin karbar shawara don ci gaban ilimi.

Haka Kuma Dr. Yusuf Kofar Mata, ya ce gwamnati na duba yuwar dawo da tsoho sunan Jami’ar Yusuf Maitama Sule zuwa Northwest, Ya godewa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa nada shi a matsayin Kwamishina tare da yabawa Tsohon gwamna Dr. Rabiu Musa Kwankwaso bisa gwagwarmayar kawo canji.

Da yake jawabi a madaddin ma’aikata, Babban Sakatare Alh. Dahiru Adda’u, ya nuna farin ciki da samu Dr. Kofar Mata a matsayin Kwamishina na Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi ya kuma bayar da tabbacin hadin kan ma’aikatan domin samun nasara.

Dan majalisa Taraya Mai wakiltar Kura da Garun Malam da Madobi, Alh. Yusuf Datti Umar da Tsohon Minista Dr. Bala Borodo da Barayen Karaye Engr. Ibrahim Karaye na daga cikin wadanda sukai jawabai, bisa rakiyar daruruwan magoya baya maza da Mata.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *