Connect with us

Labarai

Samar da Abinci: Za Mu Rubanya Kokari Kan Noman Masara -Shugaban Manoman Masara.

Published

on

IMG 20220321 WA0098

Daga Abdullahi Alhassan Kaduna.

 

Shugaban Manoman Masara na Najeriya Alhaji Abubakar Bello Funtua, yace” zasu rubanya Noman Masara don ganin ta wadatu ga Mutane dama masana’antu samar da lta ga Mutane da ma kamfanonin don ganin kamfanonin na sarrafawa don amfani daban-daban na yau da kullum.

 

Alhaji Bello Funtua,na wan nan Jawabin ne a Kaduna a taron Kungiyar na cika shekaru 30 da kafuwa, ya ce” zamu kara yawan kadada da suke shuka masarar haka kuma zamu cigaba da koyar da mambobin mu tsarin shuka irin na zamani tare kuma da nuna musu mahimmanci rungumar tsarin yin amfani da dabaru na hanyar zamani.

 

Ya kuma kara da cewar duk da matsalar tsaro da ƙasar nan ke fama da lta musamman ma yankin Arewa wanda hakan ya kawo tauwaya ga samar da Masarar don amfanin Mutane da ma kanfanoni, zamu cigaba da ganin har akai ga ana fitar da Masarar gama kasashen ketare.

 

Alhaji Abubakar Bello Funtua,ya kuma yabawa Babban bankin Najeriya dama kananan bankunan yan kasuwa kan goyon baya da suke basu kan wan nan tsari na tallafawa bangaren Manoman Masara.

 

Shi kuwa a nashi Jawabin Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-rufai,wanda Kwamishinan Noma da raya Gandun Daji na Jahar Kaduna ya wakilta, Mallam Hassan Ibrahim,yabawa Kungiyar yayi kan yunkurin ta na ganin an samar da Masarar don amfanin Mutane da ma kanfanoni.

 

Inda ya kara da cewar Gwamnatin jahar Kaduna a shirye take na ganin tayi tsare tsare da zasu habbbaka aiyukan Noma dama raya karkara, inda yace gwamnatin a shirye take na ganin sun tallafawa Noma ko wani iri ne bama kawai na Masara ba ko wani iri ne don wadata jihar dama kasar baki daya.

 

Da yake zantawa da manema labarai yayin wannan nan taron, Alhaji Abubakar Danfulotti Sokoto, nuna bukatar sa yayi na ganin gwamnatoci na bawa harkar Noma Muhimmanci don wadata kasa da abinci inda ya kara da cewar duk ƙasar da bata lya ci da kanta to fa matalauciyar kasa ce.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *