Connect with us

Labarai

Sanata Barau Jibriin na ci gaba da rabon Tallafin karatu ga daliban Jami’o’i

Published

on

IMG 20231006 WA0107

IMG 20231006 WA0108

Sanatan Kano ta Arewa Kuma mataimakin shugaban majalisar Dattawan Najeriya sanata Barau I Jibrin ya raba tallafin karatu ga daliban Jami’ar kimiyya da fasaha ta Alko Dangote dake Wudil domin karfafa musu gwiwar ci gaba da karatu yayin da ake fuskantar matsin rayuwa

Rahotanni sunce dalibai 2141 ne aka mikawa kwamitin tantancewa domin basu Tallafin, a aiki da aka fara yau Juma’a Kuma ake sa ran kammalawa a gobe Asabar.

IMG 20231006 WA0109

A yayin rabonn Tallafin, sanata Barau Jibriin ya shawarci shugabanni da mawadata su rika bada kulawa ta musamman ga bangaren ilimi kasancewar sa kinshikin gina ci gaban kowanne fanni na rayuwarc Dan Adam.

Barau Jibrin wanda ya sami wakilcin shugaban ma’aikatan sa farfesa Muhammad Ibn Abdullahi a yayin rabon tallafin, yace wannan ci gaba ne na rabon tallafin da aka faro daga jami’ar Bayero Inda dalibai Dari 6 da Hamsin suka amfana da Yusuf maitama Sule Inda dalibai 870 suka amfana a kwanakin baya.

IMG 20231006 WA01131

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *