Connect with us

Labarai

Sarkin Kano Ya Hori Al’umma Kan Dashen Itatuwa Don Yaki Da Hamada

Published

on

IMG 20230714 WA00361

Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci al’umar jihar dama kasa baki daya su himmatu wajen dasa itatuwa don kaucewa kwararowar hamada.

Mai Martaba Sarkin ya bukaci hakan ne lokacin da yaKe karbar ayarin shugabanin gudanarwa na Hukumar Kula da dazuzzuka da kwararowar hamada ta kasa karkashin jagorancin mataimakin shugaban hukumar Alhaji Auwalu Inusa Yusuf da suka kawo masa ziyara a fadarsa.

Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana cewa ya zama wajibi ga al’umar kasar nan musamman manoma dasu kaucewa sare itatuwa barkatai ba bisa ka’idaba.

Shima a nasa jawabin mataimakin shugaban hukumar Alhaji Auwalu Inusa Yusuf, yace sun Kawo wannan ziyarar ne domin gaisuwar bangirma tare da Neman tabarakin Sarki duba da cewa wannan rana ce ta bikin dashen itatuwa ta duniya Wanda ake gudanar da ita a duk shekara kuma a fadin duniya.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *