Connect with us

Labarai

Sarkin Kano Ya Shawarci Gwamnati Kan Ayyukan Hukumar Kare Haddura Ta Kasa

Published

on

IMG 20230726 WA02011

Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya shawarci gwamnati ta amincewa hukumar kare haddura ta kasa ta gudanar da aikinta a kowanne titi ba tare da takura musu ba.

Sarkin ya bayyana haka ne a yayin da yake karbar ayarin shugabanin gudanarwar hukumar kare haddura ta kasa reshen jihar Kano karkashin jagorancin sabon kwamandan hukumar Alhaji Ibrahim Abdullahi Sallau a fadarsa.

Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ce sahhalewa hukumar zata kara mata karfi wajen bincikar takardun motoci masu inganci da marasa inganci.

Mai martaba sarkin na Kano ya kuma yi kira ga direbobi da sauran masu ababan hawa su bawa hukumar kare haddura cikakken hadin kai da goyon baya don samun nasarar ayyukan hukumar.

Shima a nasa jawabin sabon kwamandan hukumar Alhaji Ibrahim Abdullahi sallau yace ya Kawo wannan ziyarar ne domin gaisuwar bangirma da gabatar da kansa a matsayin sabon kwamandan hukumar FRSC.

A wani cigaban kuma Mai Martaba Sarkin ya karbi bakoncin shugabanin gudanarwar Bankin musulinci na Jaiz karkashin jagorancin shugaban gudanarwar bankin Alhaji Muhammad Mustapha Bintube a fadarsa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *