Connect with us

Labarai

Sarkin Kano ya ziyarci tsohon shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari

Published

on

IMG 20230613 WA0101

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP ya taya Tsohon shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari murnar kammala wa”adin mulkinsa lafiya.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya ziyarci tsohon shugaban kasar ne a gidansa dake Daura domin yi masa fatan alheri sakamakon wa’adinsa da ya kare a zangon mulkinsa.

Mai Martaba Sarkin na Kano yace a mulki irin na babbar kasa Tarayyar Najeriya kuma Buharin yayi shekara takwas yana gudanar da mulki abun a tayashi murna ne kamar yadda ya fara lafiya kuma ya kammala lafiya.

Yace a tsawon shekara Takwas dole ayi dai dai ko akasin haka, adon hakane yayi fatan samun rahama da yafiyar ubangiji Allah.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *