Connect with us

Labarai

Sauke shugabanin tsaro da sauran ma’aikatu da shugaban kasa ya yi abune mai kyau–Amb,Rabi Garba Dangizo

Published

on

IMG 20230620 WA0005

….muna kyautata zaton Tinubu zai taimakawa mata zirhan kamar yadda yake da wannan kudurin..

Daga Rabiu Sanusi

Anbayyana matakin da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya dauka na sauke shugabanin tsaro da masu bada shawara ga gwamnatin sa nada kyau.

Wannan na zuwa ne daga bakin shugabar kungiyar PAPSA ta Hajiya Rabi Garba Dangizo a wata zantawa da manema labarai ta kafar sadarwa ta Whatsapp data yi a ranar litinin din nan.

Amb,Rabi Garba Dangizo tace lallai yanzu ne al’ummar kasar nan zasu tabbatar sun samu shugaban kasa kasancewar sa mai kishin talakkawa da yayi amfani da dukiyar sa wajen hidimtawa al’umma ma balle yanzu da ubangiji yabashi shugabancin kasa baki daya

Dangizo ta kara dacewa abinda tsohuwar gwamnati shugaban Buhari ta gagara to kenan tun farko data so wanda ya cigaba da basu matsala da yanzu Bola Tinubu ya ke san kaucewa mawa tare da nada wadanda yake ganin sun dace su jagoranci dukkan guraren da aka rushe dan yima jama’a aiki kamar yadda yakamata.

“Yawamcin abinda yaba tsohon shugaban kasa matsala kenan shine rashin canza wadannan shugabanin tsaro da sauran hukumomi da ma’aikatun gwamnati.”

Shugabar ta Progressive Arewa People support Asiwaju ta tabbatar da batun sauke shugabanin ma’aikatun gwamnati dana bangaren makarantu mallakar gwamnati zai taimaka matuka wajen kawo gyara ta fuskar da shugaban Tinubu ya kware da basirar sa.

DG PAPSA ta cigaba da bayyana cewa yakamata dukkan wanda za’a Dora a guraren da gwamnati ta rushe shugabancin dasu zama masu kishin talakkawa tare da bada hadin Kai ga shugaban kasa dan Samar da cigaba mai dorewa ga al’umma baki daya.

Sannan Hajiya Rabi ta tabbatar da irin goyon bayan da matan arewa da sauran na kudu suke Kara ba wannan gwamnatin shugaban kasa Tinubu wajen ganin an maido da Martabar kasar nan kamar yadda take.

Hakan nan ma ta kara da bayanin yadda shugaban kasa na yanzu yayi alkawarin tallafama mata ta fuskoki daban daban dan haka kada mata suyi kasa agwuiwa wajen addu’o’in da zasu sa ayi nasara.

Hajiya Rabi ta Kuma ayyana cewa tasan Tinubu mutum ne mai rikon amana da gaskiya,tare da kokarin ganin ya taimaki al’ummar kasar nan musamman mata dan haka take kallon lallai akwai nasarori masu tarin yawa da mata zasu amfana nan gaba kadan.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *